Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a Bangaren Rediyo da Talabijin.
Najeriya, kamar Sauran kasashe dake fadin Duniya, tana kokarin magance cutar nan ta Korona data kunno kai, bazato ba tsammani kuma keci gaba da yaduwa. Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta dauki wasu matakai don rage Illar cutar kan Mutanen Najeriya.
Don kare yaduwar cutar data shigo Najeriya, Tuni Shugaban yabada Umarnin katse zirga zirgan kasashe Goma sha Ukku 13 zuwa Najeriya, Wanda dukkan Kasashen an tabbatar da samun masu dauke da cutar ta korona (Covid-19) sama da mutum Dubu daya 1000, Gwamnati takuma dakatar da takardan Shiga kasar Visa ga wadannan kasashe, Katse Zirga zirgan zai fara aiki ne a ranar 20 ga watan ukku har sai abinda hali yayi. Dukkan Najeriya kasa ce dake son marabtan Sauran kasashen Duniya, amma kuma dole ne tabai fifiko kan kare Lafiyar Al'umman ta dakuma kasar.
Hukumomin Gwamnati daban daban dasuka hada da kafafen yada labarai Mallakan Gwamnati sun fara gangamin wayar da kai kan daukan matakan tsaftace Muhalli. Yanzu haka An kuma saurara matakan bincike a dukkannin Mashigan kasar ta sama ko ta ruwa.
Kokarin da Najeriya keyi kamar yadda aka sani, tuni har kasar tasamu yabo daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).
Fadar Shugaban kasa tana mai kara tabbatar wa 'yan Najeriya cewar Gwamnati nayin dukkan wani abu daya kamata kan Al'amarin. Babu wani abinda zaisa a tsorata, kawo yanzu matakan da aka Shimfida suna aiki yadda yakamata. An yaba sosai kan abinda kasar keyi.
Shugaban kasa yayi Na'am da aiyukan Ma'aikatu daban daban na Gwamnatinsa dakuma hukumomin Cibiyar Magance Cututtuka ta kasa (National Centre for Disease Control (NCDC), Wanda suke bashi bayanan halin da ake ciki da kuma bada shawara a matsayin kwararru.
Wa'annan Jami'an sun kafa tarihi kan gudanar da aiki cikin kwarewa.
Shugaban ya Umarci Kamfanin Mai na kasa NNPC daya rage kudin litar Man fetur. Annobar cutar ta Korona Covid-19 yayi sanadiyar rugujewar farashin Danyen Mai a kasuwan Duniya, Shine Shugaban ya yanke hukunci cewa a rage farashin na mai don kowani dan Kasar ya mora. Shine daga bisani Kamfanin Mai NNPC ta fidda sanarwa na zabtare naira 20 Wanda yanzu ake sayar wa naira 125 kan kowa ne litar a Maimakon tsohon farashi na Naira 145.
Babban Bankin Najeriya CBN, ranar Litinin ya fidda nasar kan samar da naira Tiriliyan Daya da Biliyan Daya kudin Rance ga 'yan kasuwar da annobar cutar ta shafi kasuwancin su. Bankin yakuma kafa wani tsari ga kanana da matsakaitan 'yan kasuwa, dakuma rage ribar da ake zabtarewa na Bashi, daga kaso Tara 9 zuwa kaso Biyar 5 cikin Dari.
Bamu Bukatar kirkiro da fargaba, Amma zamuci gaba da sanar da 'yan Najeriya Halin da ake ciki. Muna rokon duk wani Dan Najeriya daya bada hadin kai ga Gwamnati a kokarinta na yakar Cutar Korona Covid-19, dakuma biyayya ga Umarnin Hukumar kulada da Cututtuka takasa NCDC.
Muna da kwamitin Shugaban kasa Mai karfi karkashin jagorancin Sakataren Gwamnati (SGF). Wanda zamu basu dama don su gudanar da aikin su yadda ya kamata.
Muna kuma kara rokon 'yan Najeriya kada su siyasantar da wannan lokaci su dauka lokaci ne daya kamata su nuna sabanin su da Gwamnatin Jam'iyar APC daga Arewa, Kudu, Gabas da Yamma, dole ne 'yan Najeriya su hada kai su yaki wannan Musifa, batare da nuna sabanin Addini ko Ra'ayi ba.
A wannan batu, wasu masu raji kamar na sukar "Kwarewar Shugaban kasa, Kawai saboda maiyi jawabi wa kasar a Gidajen Telabijin, don haka suke ganin gazawar Membobin Gwamnati, da Majalisar kasar.
Wannan ba lokaci ne daya kamata wa'annan Mutane su siyasantar dashi ba.
Shugaba Buhari ya godewa dukkanin wa'inda ke kan gaba don yakar wannnan Cuta mai halakar wa.
Garba Shehu
Senior Special Assistant to the President
(Media & Publicity)
March 19, 2020.
No comments:
Post a Comment